Ƙungiyar Commonwealth Heritage Forum ta gudanar da shirin horas da fasahohin gine-ginen gargajiya a Gidan Makama, inda matasa masu zane, masu sana’a da ƙwararru suka koyi dabarun gini da kula da gine-ginen tarihi.
Shirin ya gudana ne tare da haɗin gwiwar National Commission for Museums and Monuments da kuma Bayero University Kano, yana mai da hankali kan kare gine-ginen laka na gargajiya da ke fuskantar barazanar ɓacewa.
Mahalarta taron sun bayar da horo kai tsaye akan gyaran gine-gine da amfani da kayan gargajiya, tare da ziyartar wuraren tarihi a Kano.
Masu shirya shirin sun ce manufar ita ce koyar da sabbin matasa dabarun da za su taimaka wajen kare tarihin gine-ginen Hausawa.
An rufe shirin da bikin ba da takardun shaida ga mahalarta, tare da halartar manyan baƙi da wakilan gwamnati da masarauta.