Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimi ga Abdullahi Umar Ganduje ya ce shiri ya fara nisa wajen jawo matsa zuwa ADC gabanin zaben 2027.
Kwanaki kadan bayan ya koma ADC, Salihu Yakasai ya ce sun yi wata muhimmiyar ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, inda suka tattauna kan yadda za a karfafa ADC gabanin zaben.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 26 ga Maris, 2026, Yakasai ya ce lamarin ya zama wani sabon mataki a tafiyarsa ta siyasa, musamman bayan Atiku ya tarbe shi cikin jam’iyyar ADC a hukumance.
Ya bayyana cewa daya daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna shi ne yadda za a jawo hankalin matasa su shiga siyasa ta hanyar shiga ADC.
A cewarsa, ya sanar da Atiku irin kokarin da yake yi na wayar da kan matasa domin su yi rajista a matsayin mambobin jam’iyyar.
Ya jaddada cewa shigar matasa cikin siyasa na da matukar muhimmanci wajen gina ingantacciyar jam’iyya mai karfi, yana mai cewa hakan zai ba su damar taka rawa wajen tsara makomar kasar nan.
Baya ga haka, ya ce sun tattauna kan wasu muhimman tsare-tsare da yake yi tare da abokan siyasarsa domin ganin ADC ta samu nasara a zaben 2027 daga sama har kasa, idan Allah Ya yarda.
Ya kara da cewa wannan ganawa ta kuma nuna alakar da ke tsakaninsa da iyalan Atiku, wadda ya ce dadaddiya ce, kuma yanzu ta koma hadin gwiwar siyasa karkashin wata sabuwar tafiya.