Rundunar ‘yan sandan Jihar Niger ta tabbatar da kama wani mutum mai shekaru 38, mai suna Hamisu Abdullahi, bisa zargin yin ihu da cewa “ba ruwa, ba wuta” yayin ziyarar Gwamna Mohammed Umaru Bago zuwa fadar Sarkin Suleja bayan sallar Idi.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa an kama mutumin ne bisa zargin ƙoƙarin tayar da tarzoma da kawo cikas ga ayyukan gwamnati yayin ziyarar Sallah.
Ya ce an kama Hamisu a ranar 20 ga Maris, 2026, sannan aka kai shi sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ke Minna, kafin daga bisani a ba shi beli yayin da bincike ke ci gaba.
Ɗan uwansa, Haruna Abdullahi, ya tabbatar da cewa an sake shi da beli a yammacin ranar Talata bayan ya kwashe kwanaki biyar a tsare.
Hamisu, wanda ma’aikacin lantarki ne kuma uba ga yara huɗu, ana zargin an kama shi ne bayan ya yi wannan ihu a fadar sarki lokacin da gwamnan ya kai ziyara.
Akwai jita-jitar cewa an kama shi ne bisa umarnin gwamnan, sai dai ba a tabbatar da hakan ba. Mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce bai da masaniya kan lamarin.
A gefe guda, ƙungiyar International Press Institute (IPI) Nigeria ta yi kira ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya gargadi Gwamna Bago kan duk wani mataki da zai iya tauye ‘yancin aikin jarida a jihar.
Ƙungiyar ta ce wasu matakan da gwamnati ke ɗauka na iya hana ‘yan jarida da kafafen watsa labarai gudanar da aikinsu yadda ya kamata.