Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAn ɗaure ƴan Najeriya 2 a kasar Ireland sakamakon damfarar da ta...

An ɗaure ƴan Najeriya 2 a kasar Ireland sakamakon damfarar da ta kai Yuro miliyan 6.17.

An yanke wa wasu ‘yan Najeriya biyu da ke zaune a ƙasar Ireland hukuncin daurin shekaru fiye da 16 gaba ɗaya, bayan samunsu da laifin hannu a wata babbar damfarar kuɗi ta duniya da hukumomi suka bayyana a matsayin “mai matuƙar hatsari da aka yi da ƙwarewa.”

Kamen da gurfanar da Francis Ogbuefi da Steven Silvester ya biyo bayan wani bincike mai zurfi da hukumar yaki da laifukan tattalin arziki ta ƙasar ta gudanar.

An yanke wa Ogbuefi hukuncin shekaru 9 a gidan yari, yayin da Silvester ya samu shekaru 7 da rabi.

Masu gabatar da ƙara sun ce mutanen biyu sun tafi daga Najeriya zuwa Ireland ne domin shiga cikin wata ƙungiyar damfara, inda jimillar kuɗin da aka haɗa da wannan laifi ya kai kusan Euro miliyan 6.17.

Ko da yake sun musanta zarge-zargen, kotu ta same su da laifi bayan shari’ar da aka yi a watan da ya gabata.

Rahotanni sun nuna cewa an samu sama da Euro miliyan 6 ta hanyar damfara iri-iri, ciki har da yaudarar soyayya da kuma saƙonnin damfara ta waya, inda aka rarraba kuɗin ta asusun bankuna da dama.

Masu bincike sun bayyana cewa mutanen biyu ne ke kula da asusun bankunan da ake amfani da su wajen karɓar kuɗaɗen da aka samu ta haram, suna kuma karɓar umarni daga sassa daban-daban na duniya.

An kuma gano bayanai a wayar Ogbuefi da ke ɗauke da cikakkun umarni kan yadda ake gudanar da aikin damfarar, ciki har da ayyukan da kowa zai yi, yawan kuɗin da ake mu’amala da shi, da kuma irin asusun da ya kamata a buɗe.

Haka kuma, ana zarginsa da umartar a buɗe asusu da sunayen ‘yan Ireland domin kauce wa zargi.

Masu gabatar da ƙara sun bayyana shi a matsayin babban mai haɗa kai tsakanin ‘yan damfara da ke aiki a wajen Ireland.
Bincike ya kuma gano wani bidiyo na mintuna tara da ke koyar da yadda ake aiwatar da damfarar, tare da hotuna da ke nuna yadda ake sarrafa harkokin a cikin wannan ƙungiya.

An ce yana karɓar kashi 20% na kuɗin da ake samu.
Haka kuma, an gano cewa Ogbuefi ya shiga Ireland ne a matsayin ɗalibi, yayin da Silvester ya taɓa rayuwa a tsarin kula da baƙi kafin daga bisani ya zama mai yawo ba tare da tsayayyen matsuguni ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments