Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci gwamnoni su ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma.
Hakan dai na kunshe ne cikin sanarwar da Gwamnoni su ƙara dagewa wajen samar da ayyukan yi da tallafa wa talakawa – Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci gwamnoni su ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma.
Hakan dai na kunshe ne cikin sanarwar da mashawarcin Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai Bayo Onanuga ya fitar a ranar Lahadi 22 ga Maris 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya yi da mataimakinsa da gwamnoni 23 a ranar Lahadi.
Tinubu ya jaddada bukatar gwamnoni su mayar da hankali kan manufofi da shirye-shiryen da za su shafi rayuwar al’umma kai tsaye, tare da daukar matakan rage tasirin hauhawar farashi.