Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciMatatar mai ta Dangote ta fara bawa ƙasashen Afirka mai.

Matatar mai ta Dangote ta fara bawa ƙasashen Afirka mai.

Matatar mai ta Dangote ta ƙara ƙarfafa matsayin Najeriya a kasuwar makamashi ta yankin Afirka, bayan nasarar sayar da tanka guda 12 na man fetur da ‘yan kasuwa suka yi, wanda jimillarsu ta kai tan 456,000 na kayayyakin mai da aka tace.

Matatar mai ta Dangote ta ƙara ƙarfafa matsayin Najeriya a kasuwar makamashi ta yankin Afirka, bayan nasarar sayar da tanka guda 12 na man fetur da ‘yan kasuwa suka yi, wanda jimillarsu ta kai tan 456,000 na kayayyakin mai da aka tace.

A cewar wata sanarwa daga kamfanin, man da aka tura ta hannun ‘yan kasuwa zuwa ƙasashe kamar Côte d’Ivoire, Cameroon, Tanzania, Ghana da Togo, na daga cikin fitar da man fetur da matatar ta fara yi tun bayan da ta kai ƙarfin aiki na ganguna 650,000 a rana a watan Fabrairu.

An sayar da kayayyakin ne bisa tsarin FOB (Free on Board) ga manyan ‘yan kasuwar duniya, domin su kai su zuwa ƙasashen da aka ambata.

Wannan nasara na nuna cewa matatar Dangote na da ƙarfin da ba kawai zai iya biyan buƙatun cikin gida na Najeriya ba, har ma ya zarce hakan.

Haka kuma, hakan na nuna yadda matatar ke ƙara taka muhimmiyar rawa wajen samar da mai mai inganci irin na Euro 5 ga yankin Yammacin Afirka—wani yanki da a baya ake raina shi wajen samar da mai mai inganci, har ma ana kai masa marasa inganci.

Ta hanyar samar da mai ga ƙasashen makwabta da sauran yankuna, ana sa ran matatar Dangote za ta taimaka wajen ƙarfafa tsaron makamashi a Yamma, Gabas da Tsakiyar Afirka, rage jinkirin shigo da mai daga nesa, sauƙaƙa farashi a kasuwannin mai, da kuma ƙarfafa dangantakar kasuwanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments