Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa matsalar tsaro ita ce babbar barazana ga tafiyar gwamnatinsa.
A cewarsa, hakan yana zama barazana kai tsaye ga ci gaba da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya, wanda ba haka aka so ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin kungiyar gwamnoni a gidansa da ke Legas, inda ya ke hutun karamar Sallah.
Shugaban ya jaddada cewa sabunta haɗin gwiwa da ƙasashen duniya tare da ƙarfafa alaƙa da gwamnatocin jihohi zai zama muhimmin mataki wajen kawo ƙarshen ta’addanci.
Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta magance rashin tsaro bayan tattaunawa da manyan jami’ai a Birtaniya.