Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMatsalolin tsaro ba zai hana aiki ba – Tinubu

Matsalolin tsaro ba zai hana aiki ba – Tinubu

Tinubu ya ce ƙoƙarin gwamnati zai ci gaba ba tare da barin rashin tsaro ya dakile shi ba.

Tinubu ya jaddada cewa duk da matsalolin tsaro, gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarinta.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta bari matsalar tsaro ta durƙusar da ƙoƙarin da take yi na magance matsalar tsaro a sassan ƙasar daban-daban tare da tabbatar da inganta tsaro da walwalar ƴan ƙasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a lokacin da mataimakinsa da ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a gidansa da ke Legas.

Tinubu ya ce “tattaunawar da na yi a lokacin ziyarar aiki da na kai Birtaniya ta mayar da hankali ne kan tsaro da jin daɗin al’umma, tare da nemo hanyoyin samun kayan aiki da tallafi daga ƙasashen waje.”

Tinubu ya ƙara da cewa ya tattauna da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron kan haɗin gwiwa wajen samar da kayan tsaro da tallafi.

Ya ce “gwamnati na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da sauran ƙasashe domin inganta tsaro, yana mai bayyana cewa rashin tsaro babbar barazana ce ga ci gaba da walwalar ƙasa.

Haka kuma shugaban ya yi gargaɗin tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya kan tattalin arziƙin ƙasa, musamman hauhawar farashin man fetur da rage ƙarfin saye.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments