Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya ayyana tsagaita wuta na kwanaki 5 da Iran, tare da...

Trump ya ayyana tsagaita wuta na kwanaki 5 da Iran, tare da cigaba da tattaunawa tsakanin su.

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar Litinin cewa ya ayyana tsagaita wuta na kwanaki biyar, tare da ci gaba da tattaunawa da ƙasar Iran domin samun cikakken warware rikicin da ke tsakaninsu.

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar Litinin cewa ya ayyana tsagaita wuta na kwanaki biyar, tare da ci gaba da tattaunawa da ƙasar Iran domin samun cikakken warware rikicin da ke tsakaninsu.

Trump ya bayyana cewa ya dakatar da shirin kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi na Iran bayan “tattaunawa mai kyau da amfani” da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, ya ce Amurka da Iran sun yi muhimman tattaunawa cikin kwanaki biyu da suka gabata, domin kawo ƙarshen gaba ɗaya rikicin da ke tsakanin su a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya ƙara da cewa: “Dangane da yadda tattaunawar ta kasance, wadda za ta ci gaba a cikin mako, na umurci Ma’aikatar Yaƙi da ta dakatar da duk wani shirin kai hare-hare kan tashoshin wutar lantarki da cibiyoyin makamashi na Iran na tsawon kwanaki biyar.”

Sai dai ya jaddada cewa wannan tsagaita wutar na wucin gadi ne, kuma zai dogara ne da yadda tattaunawar ke gudana a kwanakin da ke gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments