Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeRikicin Pakistan da Afghanistan na ɗaukar sabon salo bayan harin da ya...

Rikicin Pakistan da Afghanistan na ɗaukar sabon salo bayan harin da ya janyo asarar rayuka.

Wani babban rikici ya ɓarke bayan rahotanni sun bayyana cewa wani hari da ake dangantawa da jiragen yaƙin Pakistan ya afku a birnin Kabul na Afghanistan, inda aka ce ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Mahukuntan Afghanistan sun ce harin ya auku ne a wani asibiti, lamarin da ya jawo asarar rayukan fararen hula da dama.

Sai dai bangaren Pakistan ya ƙaryata zargin, yana mai cewa wuraren da aka kai harin ba asibiti ba ne, illa wasu maboyar ‘yan ta’adda. Wannan musayar zargi tsakanin ƙasashen biyu ya ƙara nuna tsanantar rikicin da ke tsakaninsu.

Abin da ya faru ya ƙara tayar da hankali a yankin, inda masu sa ido ke gargadin cewa irin waɗannan hare-hare na iya ƙara jefa yankin cikin rikici mai zurfi tare da barazana ga rayuwar fararen hula.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments