Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAtiku ya soki tafiyar Tinubu zuwa Ingila a yayin da ake kashe...

Atiku ya soki tafiyar Tinubu zuwa Ingila a yayin da ake kashe mutane a Maiduguri

Atiku ya nuna rashin jin dadinsa game da ziyarar Tinubu zuwa Ingila yayin da rikici ke ci gaba a Maiduguri.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana baƙin cikin sa da harin ta’addancin da ya hallaka mutane a Maiduguri, yayin da ya soki tafiyar shugaban ƙasar Bola Tinubu Birtaniya a daidai lokacin da ake alhinin harin.

Wata sanarwar da Atiku ya wallafa a shafinsa ta ce, a daidai lokacin da sojojin Najeriya ke mutuwa saboda tsoffin makaman da suke amfani da su, shugaban ƙasa Tinubu na ziyarar aiki a Birtaniya, yayin da a Borno ake kwashe sassan mutanen da suka mutu sakamakon kazamin harin ƙunar baƙin wake.

Atiku ya ce ya dace Sarkin Birtaniya ya san baƙon sa ya bar wasu sabbin maƙabartu da matan dake kuka saboda mutuwar mazajen su, domin zuwa wurin sa inda zai yi murmushi a gaban na’urorin ɗaukar hoto.

Tsohon mataimakin shugaban ya ce yayin da shugaba Tinubu ya bai wa hafsoshin tsaro umarnin ɗaukar mataki, su kuma ƴan ta’adda sai suka aike da ƴan ƙunar baƙin wake, kuma ƴan Najeriya sun ga ko wanene ke samun nasara.

Atiku ya bayyana gwamnati mai ci a matsayin wadda ta ɗauki jana’iza a matsayin abinda ya zama ruwan dare, yayin da sukar ta kuma ya zama cin amanar ƙasa, saboda haka ta gaza hurumin ci gaba da jagoranci.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya shaidawa gwamnati mai ci cewar ba za ta yi kamfen na zaɓen shekarar 2027 a kan kaburburan jama’a ba, waɗanda ta gaza kare rayukan su.

Yayin da ya buƙaci sake dabarun yaƙi da ta’addanci a ƙasar, Atikun ya kuma jinjinawa jami’an tsaron dake sadaukar da rayukan su, yayin da ya zargi gwamnati da mayar da hankali wajen murƙushe ƴan adawa kawai.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments