Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya ce Amurka ta kai mummunan harin bama-bamai kan Iran

Trump ya ce Amurka ta kai mummunan harin bama-bamai kan Iran

Donald Trump ya sanar da cewa Amurka ta kai hari mafi tsanani kan Iran.

Yayin da yakin da ake gwabzawa a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila ke cigaba da daukar zafi bayan Donald Trump ya sanar da kai hari tsibirin Kharg.

Hakan na zuwa ne bayan shiga mako na biyu da fara yakin da Amurka,Isra’ila suka kaddamar a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Donald Trump ya ce zai cigaba da kai hari tsibirin Kharg matukar Iran ta cigaba da toshe mashigar Hormuz.

Donald Trump ya ce ya aiwatar da daya daga cikin manyan hare-haren bama-bamai mafi karfi a tarihin Gabas ta Tsakiya, inda ta lalata gaba dayan wuraren soja da ke tsibirin Kharg na Iran.

Trump ya kuma bukaci Iran ta ajiye makamanta, tana mai cewa idan ta yi haka za ta tsira da sauran abin da ya rage bai lalata ba a kasar.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments