Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAmurka ta nemi bayanai kan Mojtaba Khamenei tare da sanya ladan Dala...

Amurka ta nemi bayanai kan Mojtaba Khamenei tare da sanya ladan Dala miliyan 10

Amurka ta yi alkawarin Dala miliyan 10 ga duk wanda ya ba da bayanai kan Mojtaba Khamenei.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ladan Dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan wajen da sabon shugaban addinin Iran Mojtaba Khamenei da wasu manyan jami’ai su ke.

Ministan Harkokin Cikin Gidan Iran Eskandar Momeni da Ministan Leken Asiri da Tsaro Esmail Khatib na cikin mutane 10 da ke cikin jerin sunayen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana da nemansu ruwa ajallo.

Wannan dai na zuwa ne, yayin da Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce sun raunata sabon shugaban addinin na Iran a hare haren da suke kai wa ƙasar.

Sai dai a ranar alhamis shugaban ya gabatar da takardar jawabi da aka karanta ta a kafar talabijin, inda ya bayyana shirin ci gaba da rufe mashigar ruwan Hormuz da kuma gabatar da buƙatar korar sojojin Amurka daga yankin Gabas ta Tsakiya.

Cikin wata sanarwa da Ma’aikar harkokin Wajen na, Amurka ta fitar jiya Jumma’a, ta ce waɗannan mutane na jagorantar sassa daban-daban na Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), waɗanda ke tsarawa tare da, aiwatar da ta’addanci a duk faɗin duniya,”

Sanarwar ta ce bayaga bada lada ga duk, wanda ya bada bayanai a kan jami’an na Iran, za’a kuma bashi kariya ta musamman, ko da kuwa ya bukaci yin rayuwa a wajen Iran.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments