Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeChina ta ba wa Iran tallafin makudan kudade

China ta ba wa Iran tallafin makudan kudade

China ta tallafawa Iran da kudade masu yawa ga daliban da aka kashe yayin harin makami mai linzami.

Gwamnatin China ta sanar a ranar Juma’a 13 ga watan Maris, 2026 cewa za ta ba da tallafin kudi ga Iran.

Kasar China ta bayyana cewa za ta bayar da tallafin $200,000 ga iyalan daliban da aka kashe a harin makami kan wata makaranta a Iran.

Beijing ta bayyana harin a matsayin wanda aka kai ba tare da tantancewa ba, yana mai cewa ya faru ne a farkon rikicin da ya barke a Gabas ta Tsakiya, cewar Al Jazeera.

Gwamnatin Iran ta zargi Amurka da Isra’ila da kai harin makamin da ya afkawa makarantar da ke kudancin kasar a ranar farkon yakin.

Rahotannin kafafen yada labarai na Iran sun ce an gudanar da jana’izar akalla mutane 165 da suka mutu a harin, daga ciki har da yara

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba ta wata hanya mai zaman kanta.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments