Iran ta kai hari ofishin jakadancin Amurka a Baghdad na ƙasar Iraki.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sojojin ƙasar sun lalata sansanin sojojin Iran a Tsibirin Kharg, wanda ke bakin tekun kudu maso Yammacin Iran, inda ya yi gargadin cewa nan gaba ƙadan za su fara kai hari a kan albarkatun man iran da ke yankin.
Trump ya ce da gangan Washington ta kare kayayyakin man fetur na tsibirin, amma ya yi gargadin cewa za su iya kai mata hari idan Iran ta tsoma baki a harkokin jigilar kaya ta mashigin Hormuz.
Sai dai, Tehran ta yi gargadin cewa duk wani hari da aka kai wa cibiyoyin makamashinta, to ko shakka babu akwai ramuwar gayya ga kayayyakin more rayuwa na yankin da kuma kadarorin masu alaka da Amurka a yankini, wanda hakan ke kara fargabar barkewar rikicin makamashi da tsaro a fadin yankin Gulf.
Isra’ila ta kai wani mummunan hari babban birnin Iran daidai lokacin da dubban mutane suka taru ranar Juma’a domin gudanar da gangami na shekara-shekara da gwamnati na goyon bayan Falasdinawa da kuma yin kira ga kawo karshen Isra’ila.
A nata bangaren, Iran ta kai hari Ofishin jakadancin Amurka da ke Baghadaza na kasar Iraki da safiyar wannan Asabar.