Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAkwai yiwuwar farashin tikitin jirgi ya ƙaru a Najeriya – Masana

Akwai yiwuwar farashin tikitin jirgi ya ƙaru a Najeriya – Masana

Masu tafiye-tafiye na iya fuskantar ƙarin kuɗin tikitin jirgi a Najeriya.

Farashin tikitin jirgin sama na iya karuwa a Najeriya bayan tashin gwauron zabo da farashin man jirgin sama na Jet A1 ya yi.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa a halin yanzu ana sayar da litar man da kusan N1,835 a Kano, N1,820 a Abuja, N1,815 a Port Harcourt da kuma N1,780 a Lagos, yayin da kafin barkewar yakin Iran ana sayar da litar man jirgin a kusan naira 1,000.

Sai dai masana harkar sufurin sama sun gargadi cewa wannan karin kudin man na iya tilasta kamfanonin jiragen sama su kara farashin tikiti domin daidaita kudaden aiki.

Sun kara da cewa hakan na iya rage yawan mutanen da ke yin tafiye-tafiye ta jirgin sama, musamman wadanda tafiyarsu ba ta da matukar muhimmanci.

SourceIconic
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments