Sojin Faransa guda daya ya mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin jirgi marar matuƙi kan sansanin Sojin haɗakar ƙasashen Turai da Amurka da ke yankin Erbil na Kurdistan an Iraqi.
Harin dai wanda ke zuwa a kwana na 15 da faro yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran, bayanai sun ce ƙungiyoyin da ke biyayya ga Iran a cikin ƙasar ta Iraqi ne suka ƙaddamar da shi wanda ya yi gagarumar ɓarna a sansanin Sojin.
Wannan shi ne asarar rai na farko ko kuma jikkatar sojoji da Faransa ta fuskanta tun bayan faro wannan yaƙi a ranar 28 ga watan fabarairun da ya gabata.
Shugaba Emmanuel Macron da kansa ya sanar da kisan Sojan, wanda ya yi bayyana da cewa ba abin lamunta ba ne.
Tun gabanin wannan hari da sanyin safiyar yau Juma’a Italiya a jiya Alhamis ta sanar da shirin janye dakarunta daga sansanin wanda ke an Iraqi, bayan wani harin jirgi marar matuƙi da bai jikkata kowa ba.
A jawabin da ya gabatar gaban manema labarai ministan tsaron Italiya Guido Crosetto ya ce janye dakarun na wucin gadi kasancewar za su koma sansanin sojin na haɗin gwiwa da ke yankin na Kurdistan bayan lafawar lamurra a yankin na gabas ta tsakiya.
Harin na safiyar yau ya zo ne bayan jawabin sabon jagoran addinin na Iran Ayatollahi Mojtaba Khamne’i da ke cewa suna da yaƙinin ƙungiyoyin da ke mara musu baya a Iraqi da Yemen da kuma Lebanon za su ci gaba da bayar da gudunmawa har zuwa ƙarshe.