Majalisar Dattawa ta shirya ganawa da Asusun Lamuni na Duniya IMF domin tattauna halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da shirye-shiryen gyara da ake aiwatarwa a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu.
Wannan dai wata tattaunawa ce da ake gudanarwa tsakanin IMF da Najeriya a kai a kai domin tantance manufofin tattalin arziki da kwanciyar hankalin kuɗi a ƙasar.
Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa,Barau Jibrin ne ya sanar da taron da za a gudanar daga 4 ga Maris zuwa 17 ga Maris, 2026.
Ana sa ran wannan ganawar zai bai wa ‘yan majalisar damar fahimtar tsarin sarrafa tattalin arzikin gwamnati da kuma gano irin goyon bayan da wannan Asusun Lamuni na Duniya zai iya bayarwa wajen aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arzikin Tarayyar Najeriya.