Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeJirgin yaƙin Amurka ya kife bayan hatsari a Iraƙi

Jirgin yaƙin Amurka ya kife bayan hatsari a Iraƙi

Jirgin sojin Amurka ya faɗi a ƙasar Iraƙi.

Wani Jirgin rundunar sojin Amurka ya gamu da hatsari a cikin ƙasar Iraƙi, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta tabbatar da faruwar lamarin.

Jirgin sojin na KC-135 ya faɗo ne bayan wani hatsarin da ya shafi wasu jirage biyu.

Rundunar sojin Amurka ta ce “ana ci gaba da aikin ceto” a yammacin Iraƙi – abin da sojoji suka ce ya faru ne a “yankin da ba na maƙiya ba.”

“Lamarin dai ba a yankin da ake yaki ya faru ba ko kuma musayar wuta,” in ji sanarwar.

Jirgi na biyu da lamarin ya shafa ya sauka lafiya, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments