Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBabu wani dan siyasa dake karkashi na da zai zama barazana ga...

Babu wani dan siyasa dake karkashi na da zai zama barazana ga dimokuraɗiyya – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa a ƙarƙashinsa da zai iya zama barazana ga dimokuraɗiyya ko dokar ƙasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taron buɗe-baki da shugabannin jamʼiyyun siyasa a Fadar shugaban ƙasa.

Ya ce, “Ni dan ga-ni-kashe-nin dimokuradiyya ne.

Masu rinjaye za su samu abin da suke so, marasa rinjaye ma za su samu abin da suke so, siyasa ta fi daɗi idan kai ne ke samun nasara.”

Shugaban ya nanata cewa dokar ƙasa da dimokuraɗiyya za su ci gaba da zama ginshiƙai masu ƙarfi a mulkinsa.

Tinubu ya kuma jaddada cewa ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin jamʼiyyu abu ne mai muhimmanci domin gina tsarin zabe da cibiyoyi masu gaskiya.

Shugaban ya kuma bayyana cewa dole ne dokar ƙasa ta yi mulki a kowace dimokuraɗiyya inda ya tabbatar wa shugabannin jam’iyyu cewa za a gudanar da zabuƙa cikin gaskiya a ƙarƙashin mulkinsa.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments