Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAmurka ta ba wa Rasha izinin sayar da man Rasha don sauƙaƙa...

Amurka ta ba wa Rasha izinin sayar da man Rasha don sauƙaƙa hauhawar farashin mai

Amurka ta sassauta dokoki kan man Rasha domin rage hauhawar farashin mai.

Gwamnatin Amurka ta bayar da umarnin sayar da man Rasha na wucin-gadi, da cewa ta yi hakan ne da nufin magance karanci da tsadarsa a duniya.

Masu sayen man dai sun nuna damuwa kan yadda farashin ke tashi, kuma bayan ga haka a karshe ma zai shafi farashin sauran kayayyaki.

Ya zuwa jiya Alhamis Baitul-malin Amurka ya amince da bayar da lasisin sayar da mai da kayayyakin da aka yi da man wadanda tuni aka loda a jiragen ruwa.

An yi hakan ne kwana daya bayan kasashe 32 da hukumar makamashi ta duniya ciki har da Amurka suka amince su, saki ganganr mai miliyan 400.

To amma kuma duk da wannan mataki na hukumar, farashin man ya ci gaba da tashi a jiya Alhamis, inda man samfurin Brent ya zarta sama da dala dari daya a ganga daya a karon farko tun 2022.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments