Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBankin Citi ya bayyana cewa zai rufe dukkan ofisoshinta a Hadaddiyar Daular...

Bankin Citi ya bayyana cewa zai rufe dukkan ofisoshinta a Hadaddiyar Daular Larabawa sai ɗaya kawai ne zai zama a buɗe bayan Iran ta yi barazanar kai hari kan bankuna a yankin

Bankin ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan yanayin kasar da ya canza.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa Bankin ya umarci ma’aikatanta su bar ofisoshinsu su sanna su yi aiki daga gida har sai an ba da ƙarin umarni.

Rahoton ya ƙara da cewa bankin Standard Chartered ma ya fara fitar da ma’aikatansa daga ofisoshin su na Dubai.

Wadannan matakai dai sun biyo bayan wani jawabi daga kakakin rundunar Khatam al-Anbiya na Tehran, inda aka ce Iran za ta kai hari kan harkokin tattalin arziki da bankuna da suka shafi Amurka da Isra’ila a yankin, bayan harin da aka kai wani bankin Iran.

Hakazalika, bankin HSBC ya sanar a wata sanarwa ta daban cewa ya rufe dukkan ofisoshinsa a Qatar har sai an ba da ƙarin umarni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments