Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Iqamatissunnah (JIBWIS) ta sanar da dakatar da tafsirin watan Ramadan da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ke gabatarwa a Masallacin Mokas da ke Damaturu, Jihar Yobe.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na JIBWIS NHQ Jos-Damaturu, kungiyar ta bayyana cewa an tura malamin ne daga hedikwatar ta ta kasa da ke Jos, kamar yadda aka saba yi tsawon shekaru 35 da suka gabata, inda ake aikewa da malamai daban-daban domin jagorantar tafsirin watan Ramadan a yankin.
Sanarwar ta ce a bana (1447H/2026), Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya fara gabatar da tafsirin tun daga farkon watan Ramadan, inda ya shafe kwanaki 11 yana gudanar da darussa. Sai dai a ranar 12 ga watan Ramadan aka dakatar da shi bisa umarnin Shugaban Majalisar Malamai na Kasa, Muhammad Sani Yahya Jingir, sakamakon dalilan tsaro.
A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan wasu hudubobi da nasihohi da malamin ya gabatar, ciki har da wa’azi a hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Yobe a ranar Juma’a, da kuma nasiha da ya yi da asuba a Masallacin Alimarami a ranar Asabar.
Haka kuma, an bayyana tafsirin da ya gabatar a daren Juma’a a Masallacin Mokas, inda aka ce ya sanya kayan agaji yayin da yake bayani.
Sanarwar ta ce batutuwan da ya tabo sun shafi bangarori daban-daban na al’umma, ciki har da jami’an tsaro, gwamnoni da ma Shugaban Kasa.
Kungiyar ta bayyana cewa salon da malamin ya yi amfani da shi musamman wajen ambaton sunayen wasu mutane tare da yin tsinuwa da jafa’i ya sabawa tsarin koyarwar JIBWIS, wadda ta tanadi wa’azi da nasiha cikin hikima, ladabi da tsari.
A ranar 14 ga Ramadan 1447H, Shugaban Majalisar Malamai na Kasa ya kira taro da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria, tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Yobe da kuma wakilai uku daga Karamar Hukumar Damaturu.
A yayin taron dai, an bai wa kowane bangare damar gabatar da nasa jawabi kafin a yanke hukunci kan lamarin.