Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiRonaldo ya yi gudun hijira daga Saudiyya zuwa Madrid kan rikicin Gabas...

Ronaldo ya yi gudun hijira daga Saudiyya zuwa Madrid kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Yayin da birnin Riyadh na Saudiyya ke fuskantar hare-hare daga Iran, rahotannin sun tabbatar da cewa jirgin alfarma na gwarzon ɗanwasa Cristiano Ronaldo, ya tsere tare da ɗanwasan a ciki zuwa birnin Madrid na Sifaniya.

Ɗan asalin Portugal, Ronaldo na buga wa ƙungiyar Al Nassr da ke da mazaunin a Riyadh babban birnin Saudiyya, inda ko a ranar Litinin sai da aka kai hari kan pfishin jakadanci na Amurka.

Yayin da aka shiga rana ta huɗu ta Amurka da Isra’ila suka fara kai wa Iran hari, inda Iran ta fara kai harin ramuwa kan sansanonin sojin Amurka a ƙasashen yankin Gulf irin su Saudiyya, da Qatar, Bahrain, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Sakamakon caɓewar lamura a yankin na Gabas ta Tsakiya, al’ummomin ƙasashen waje suna ta tserewa daga yankin don kaucewa rikicin.

Ronaldo da abokiyar zamansa, Georgina Rodriguez da kuma ‘ya’yansu biyar suna zama a Riyadh. Kuma ganin cewa yana da jirginsa na kansa, ana raɗe-raɗin shi ma ya bar Saudiyya ya tafi Turai.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments