Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAPC ta tanadi kwamitin da zai sa ido kan zaɓen shugabanta a...

APC ta tanadi kwamitin da zai sa ido kan zaɓen shugabanta a Kano da za a gudanar a yau.

An nada kwamitin da zai jagoranci zaɓen shugaban APC a Kano, wanda aka tsara yi yau Talata.

Jam’iyyar APC a Kano ta samar da kwamitoci uku wadanda za su kula da yadda za a gudanar da babban taron jam’iyyar na jiha, wanda za a yi a yau Talata.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na Kano Ahmad S Aruwa ya fitar, inda ya ce za’a gudanar da taron ne a dakin wasa na Kofar Mata da karfe takwas na dare.

Sanarwar ta ce an kafa kwamitocin ne domin tabbatar da gaskiya da adalci tare da tsari mai kyau, daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da dokokinta yayin zaben fitar da sabbin shugabanni.

Kwamitocin dai sun hada da Kwamitin gudanarwa da tantance wakilai karkashin jagorancin Rabi’u Sulaiman Bichi, da kuma Kwamitin yada labarai karkashin jagorancin Muhammad Garba.

Haka kuma akwai kwamitin tsaro da ke karkashin jagorancin Kanal Malami domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin gudanar da taron.

Kakakin jam’iyyar ya bayyana cewa shugabancin APC na Kano na da cikakken yakini kan kwarewar kwamitocin wajen tabbatar da an gudanar da taron cikin lumana da nasara.

Ya kuma bukaci ‘ya’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki su ba da hadin kai tare da bin doka da oda.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments