Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmurka ta bukaci ‘yan ƙasarta da ke yankin Gabas ta Tsakiya su...

Amurka ta bukaci ‘yan ƙasarta da ke yankin Gabas ta Tsakiya su bar wurin cikin gaggawa.

Amurka ta ce ya zama dole ‘yan ƙasarta su fice daga yankin Gabas ta Tsakiya nan take.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta gargadi ‘yan ƙasarta da su fice daga yawancin ƙasashen Gabas ta Tsakiya, tana mai nuni da “mummunan barazanar tsaro” da ke ƙara tsananta a yankin.

A cikin wata sanarwar tsaro da ta fitar a ranar Litinin, ma’aikatar ta lissafo ƙasashen da gargadin ya shafa da suka haɗa da Bahrain, Egypt, Iran, Iraq, Israel, yankunan Gabar Yamma da Gaza da aka mamaye, Jordan, Kuwait, Lebanon, Oman, Qatar, Saudi Arabia, Syria, United Arab Emirates da kuma Yemen.

Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin jakadanci, Mora Namdar, ta wallafa a shafinta na X tana kira ga Amurkawa da su “FICE YANZU” daga wuraren da aka ambata ta hanyar amfani da jiragen kasuwanci da ke aiki.

Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara ruruwa a yankin, inda Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran tun daga ranar Asabar. A martanin da ta mayar, Iran ta harba jirage marasa matuƙi da makamai masu linzami kan Isra’ila da kuma kadarorin Amurka a yankin.

⁩

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments