Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu ta ƙi amincewa da buƙatar tsofaffin kwamishinonin Kano

Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar tsofaffin kwamishinonin Kano

Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar da tsofaffin kwamishinonin Kano suka shigar a kan gwamna Abba.

Kotun Masana’antu ta Ƙasa da ke zamanta a sashen shari’a na Kano ta ƙi amincewa da buƙatar wasu tsoffin ƴan majalisar zartarwa ta jihar Kano.

Tsofaffin kwamishinonin sun shigar da kara ne suna neman kotu ta dakatar da gwamnati daga kwace motocin da aka ba su yayin da suke kan muƙami.

Rahotanni sun bayyana cewa alƙali Mahmood Abba Namtari ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin 2 ga watan Maris, 2026 bayan nazarin buƙatun wucin-gadi da tsoffin kwamishinonin suka shigar.

Tsofaffin kwamishinonin Kano da dama ne suka shigar da korafi iri ɗaya, lamarin da ya sa kotu ta haɗa su wuri guda domin sauraro.

Sai dai alƙalin ya ƙi bayar da umarnin wucin-gadi na hana gwamnati kwace motocin, tare da umartar a saurari shari’ar bayan an bai wa dukkanin ɓangarorin damar gabatar da hujjojinsu.

Wannan na nufin ba za a hana kowa e motocin na wucin-gadi ba sai an fara jin ta bakin gwamnati da sauran waɗanda ake ƙara.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments