China ta musanta jita-jitar baiwa Iran tallafin Soji a yaƙin da ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya ke gwabzawa yanzu haka da ƙasashen Amurka da Isra’ila a lokaci guda.
China wadda ta yi kakkausar suka ga hare-haren Amurka a Isra’ila da ta kira kuskuren da ba zai gyaru ba, ta ce tana bibiyar dukkanin abubuwan da ke faruwa a ƙasar.
China dai na shigar da kashi 70 na fetur ne daga mashigin ruwan Hormuz da Iran ta kulle tun daga jiya kuma kaso mai yawa na man da Beijing ke buƙata na fitowa ne daga Iran kodayake ta kan siya daga ƙasashen Iraqi da Saudi Arabia da kuma Kuwait.
Sai dai duk da muhimmancin Iran ga China ta ce ko kusa ba ta tallafawa Tehran da kowanne nau’in agaji a yaƙin nata da Amurka ba, inda ƙasar ta nanata cewa bisa dukkanin alamu tattaunawar farko tsakanin Amurka da Iran na tafiya yadda yakamata gabanin samun matsala.
Ko a jiya Litinin sai da ministan wajen ƙasar Wang Yi ya yi wata tattaunawa da takwarorinsa na ƙasashen Oman da Iran da kuma Faransa kuma ya bayyana cewa bayanan da ya gano shi ne Amurka da Isra’ila ta gangan suka yiwa tattaunawar zagon ƙasa don shiga yaƙin.
China na ci gaba da kiran tsagaita wuta tare da hawa teburin sulhu maimakon yaƙi.
China na sahun ƙasashen da Iran ke samun taimako daga garesu, musamman ta fuskar tattalin arziƙi inda a lokuta da dama Beijing ke bayyana Tehran a matsayin ƙawa inda kuma ko da bayan wannan harin ta nanata cewa Iran na da cikakkiyar damar kare kanta.
Sai dai a cewar Wang Yi suna taimakawa Iran ne kaɗai a siyasance da kuma ƙarfafa mata gwiwa amma ba ta ɓangaren Soji ba.