Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiIran ta karyata ikirarin yin sulhu da Amurka

Iran ta karyata ikirarin yin sulhu da Amurka

Kasar Iran ta yi watsi da batun sulhu da Amurka

Jamhuriya Musulunci ta Iran ta yi watsi da ikirarin shugaban Amurka Donald Trump kan cewa ta bukaci a tattauna duk da hare-haren da su ke cigaba da kaiwa juna.

A daidai lokacin da aka shiga ƙwana na uku a jere da faro yakin, ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce dakarun kasar uku sun gamu da ajalinsu wasu biyar kuma sun samu munanan raunuka a hare-haren makami mai linzami da Iran ta kai kan sansaninta na Centcom a Gabas ta Tsakiya.

A nata bangare rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasara hallaka manyan kwamandojin sojin Iran akalla 40 da suka hada da ministan cikin gida da shugaban rundunar dakarun juyin juya halin ƙasar ba yaga jagoran addini muslunci AyatollAh Ali Khamenei da shi ma ya rasa ransa a farmakin.

A matsayin martani, dakarun rundunar kundun bala Kasar Iran IGRC ta harba makamai masu linzami a sassan Biranen Tel aviv da Jérusalem da ma wasu sansanonin sojin Amruka da ke Gabas ta Tsakiya.

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta shaida mutuwar mutane 9 yayin da wasu 11 suka ɓata sakamakon a lardin Bet Shemesh na Isra’ila sakamakon hare-haren Iran.

Haka ma jaridu a yankin sun ruwaito cewa akalla mutum hudu sun mutu yayin da wasu 58 suka jikkata bayan da Iran tayi ruwan makamai masu linzami kan biranen Doha,da Bahreïn da kuma Oman.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments