Gwamnan Jihar Neja, Muhammadu Bago ya bayyana cewa yanzu haka akwai al’ummar jihar fiye da dubu 300 da ƴan ta’adda suka tilastawa barin matsugunansu a ƙananun hukumomi 10 na jihar da ke fama da matsalolin tsaro.
Bago wanda ya sanar da alƙaluman yayin jawabinsa ga manema labarai jim kaɗan bayan karɓar tallafin jinƙai daga gwamnatin Najeriya a birnin Minna, ya bayyana cewa ɗimbin ƴan gudun hijirar na buƙatar tallafi don kaucewa faɗawarsu hannun ɓatagari.
Gwamnan na jihar Neja ya bayyana cewa adadin na mutane fiye da dubu 300 ƙiyasi ne kawai don a yanzu ne mahukuntan jihar ke kan tantance yawan mutanen da wannan matsala ta shafa.
Jihar Neja dai da ke tsakiyar Najeriya na sahun jihohin da ke ganin ƙololuwar ta’azzarar matsalolin tsaro daga mabanbantan ƙungiyoyin ta’addanci, ciki har da boko haram da Ansaru da kuma mamudawa a baya-bayan nan, baya ga ƴan bindiga.
A cewar Gwamnan Bago akwai buƙatar shigar gwamnatin ƙasar da nufin ilimantar da ƴaƴan ƴan gudun hijirar don taƙaita illar ƴan ta’addan.