Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiIran ta dauki manyan matakan tsaro bayan kashe jagoran musulunci, Khamenei a...

Iran ta dauki manyan matakan tsaro bayan kashe jagoran musulunci, Khamenei a harin Amurka

Biyo bayan mutuwar Ayatollah Ali Khamenei Iran ta dauki wasu manyan matakai

Bayan tabbatar da mutuwar Ayatollah Ali Khamenei,biyo bayan hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, gwamnatin Iran ta dauki wasu tsauraran matakai.

Imam Ayotallah Khamenei, ya rasu yana ɗan shekara 86, ya kasance jagoran ƙasar tun shekarar 1989.

Shafin Telegram na gidan talabijin na ƙasar, IRIB, shi ne ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce:

“Jagoran al’umma, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Khamenei, ya yi ‘Shahada.’

Sai dai kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun sanar da dokar yin zaman makoki na kwanaki 40 a faɗin ƙasar domin girmama Khamenei.

Wannan mataki ya haɗa da bayar da hutun kwanaki bakwai a jere, inda aka rufe dukkan ofisoshin gwamnati, makarantu, da wuraren kasuwanci, a cewar rahoton.

Dangane da tanadin kundin tsarin mulkin Iran, an kafa wata majalisar shugabanci domin jan ragamar ƙasar a wannan lokaci da ake shirin sauya shugaba.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun ɗora wa Amurka da Isra’ila alhakin harin, inda suka yi rantsuwar daukar fansa ta hanyar kai hare-hare masu tsanani.

Tuni dai Iran ta ƙaddamar da hare-haren makami mai linzami kan wasu wurare a Isra’ila da ƙasashen Gulf jim kaɗan bayan tabbatar da mutuwar Khamenei,cewar rahoton KGNS News.

A cikin gida kuma, hukumomi sun tsaurara tsaro, inda aka tura dakarun IRGC domin murƙushe zanga-zanga da kiyaye doka a daidai lokacin da ake samun hatsaniya da kuma bukukuwan murna a wasu yankuna.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments