Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya mika saƙon ta’aziyyarsa kan mutuwar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Kamfanin dillancin labaran Rasha na TASS ya ambato Shugaba Putin na bayyana kisan Khamenei da ”Kisan gillar da ya saɓa wa dokokin duniya da mutunta ɗan’adam”.
Rasha dai ta kasance babbar ƙawa ga Iran.
A shekarar da ta gabata ne ƙasashen biyu suka amince da yarjejeniyar hadin gwiwar soji.