Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiIran ta ƙaddamar da hari kan wasu muhimman wuraren sojin Amurka

Iran ta ƙaddamar da hari kan wasu muhimman wuraren sojin Amurka

Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa Iran ta yi amfani da makamai masu linzami wajen kai harin kan sansanonin Amurka.

Iran ta sake kai sabbin hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka da ke wasu kasashen yankin Yankin Golf, bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a cikin kasar Iran.

Rahotanni sun bayyana cewa an harba makamai masu linzami kan wuraren da ke dauke da makaman sojin Amurka a kasashen Bahrain, Qatar da wasu sassan yankin, lamarin da ya haddasa karar fashe-fashe tare da hayaki a wasu birane.

Ma’aikatun tsaro na wasu daga cikin kasashen sun ce sun samu nasarar dakile wasu makaman, yayin da wasu wurare suka dauki matakan kwashe jama’a domin kare rayuka.

A Bahrain dai, an bayar da umarnin ficewa daga wasu yankuna da ke kusa da sansanin sojin ruwa na Amurka, yayin da a Qatar aka ji karar wasu fashe-fashe duk da ikirarin cewa an kakkabe makaman da aka harba.

Hukumomin Iran sun bayyana cewa hare-haren wani bangare ne na mayar da martani kan abin da suka kira keta hurumin kasarsu, suna mai cewa za su ci gaba da daukar matakan kare kansu.

Wannan mataki ya kara dagula al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya, inda kasashe da dama ke kira da a dakatar da tashin hankalin tare da komawa teburin sulhu domin kauce wa fadada rikici.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments