Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, tare da wasu manyan jami’ai biyu, za su jagoranci ƙasar a lokacin rikon kwarya bayan rasuwar Jagoran Ƙoli na Iran, Ali Khamenei.
Gidan talabijin na ƙasar ya ruwaito cewa shugaban ma’aikatar shari’a, Gholamhossein Mohseni Ejei, da wani jami’i daga Majalisar Kula da Doka za su kasance cikin kwamitin mutum uku da zai kula da harkokin mulki na wucin gadi.
Rahoton ya ce wannan mataki ya biyo bayan bayanin da ɗaya daga cikin mashawartan marigayi Khamenei ya yi.
A tsarin mulkin Iran, akwai wani kwamiti na malamai 88 da ake kira ‘Assembly of Experts,’ wanda ke da alhakin zaɓen sabon jagoran ƙoli.
Wannan kwamiti ne kaɗai ke da ikon naɗa ko ma sauke jagoran ƙoli, duk da cewa ba a taɓa sauke wani ba a tarihin ƙasar.
Ana zaɓen mambobin wannan kwamiti duk bayan shekara takwas. Sai dai dole ne ‘yan takarar su samu amincewar ‘Guardian Council’, wacce ke tantancewa tare da cire wasu ‘yan takara kafin zaɓe.
Dokar Iran ta tanadi cewa dole ne Majalisar ta zaɓi sabon jagoran ƙoli a cikin gaggawa.
Amma idan aka samu jinkiri, ana iya kafa kwamitin rikon kwarya wanda zai riƙe dukkanin ayyukan jagoranci na ɗan lokaci.
Idan aka kafa irin wannan kwamitin a halin yanzu, zai ƙunshi shugaban ƙasa, shugaban ma’aikatar shari’a, da kuma wakili daga Majalisar Kula da Doka wanda majalisa ta zaɓa.
Wannan majalisa ce da ke ba jagoran ƙoli shawara tare da sasanta saɓani da majalisar dokoki.
A halin da ake ciki, hakan na nufin Shugaba Pezeshkian da shugaban ma’aikatar shari’a Mohseni Ejei za su taka muhimmiyar rawa a wannan lokaci na sauyi.
Rahotanni sun kuma nuna cewa ɗan marigayi Khamenei na daga cikin waɗanda ake ganin za su iya neman kujerar jagoran ƙoli, duk da cewa batun maye gurbin na da sarkakiya a tsarin addini da siyasar Iran.