Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya fice daga PDP

Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya fice daga PDP

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya zama gwamna na 30 da ke ƙarƙashin APC.

A cikin jawabin da ya yi wa al’ummar jihar, Fintiri ya bayyana cewa ya koma APC tare da mambobin majalisar zartarwarsa da kuma shugabannin PDP a jihar.

Ya ce an ɗauki matakin ne domin amfanin ci gaban jihar Adamawa da al’ummarta gaba ɗaya.

Sauyin sheƙar Fintiri ya zo ne makonni bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shiga APC a matsayin gwamna na 29 a jam’iyyar, bayan ya yi murabus daga NNPP sakamakon rikice-rikicen cikin gida da saɓanin shugabanci.

Da sauya shekar Fintiri, alkaluman sun nuna cewa APC na da gwamnoni 30, yayin da PDP ke da gwamnoni uku kacal.

Jam’iyyun APGA, Labour Party da Accord Party na da gwamna guda dai-dai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments