Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta ce ta kwato motocin gwamnati daga wasu tsofaffin kwamishinoni da suka yi murabus daga majalisar zartarwa ta jihar.
A cewar hukumar, jami’anta sun gudanar da aikin kwato motocin ne a ranar Alhamis bayan zargin cewa wadanda abin ya shafa sun ƙi mayar da kadarorin gwamnati duk da umarnin da aka ba su.
Daga cikin tsofaffin kwamishinonin da abin ya shafa akwai Air Vice Marshal Ibrahim Umar (mai ritaya), tsohon kwamishinan tsaron cikin gida; Mustapha Rabiu Kwankwaso, tsohon kwamishinan matasa da wasanni; Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, tsohon kwamishinan kimiyya da fasaha; Dakta Adamu Aliyu Kibiya, tsohon kwamishinan harkokin jin kai; da Hon. Nasiru Sani Garo, tsohon kwamishinan ayyuka na musamman.
Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, wanda ya jagoranci aikin, ya shaida wa manema labarai cewa sun dauki matakin ne bayan wadanda abin ya shafa sun gaza bin umarnin mayar da motocin gwamnati da ke hannunsu.
Ya ce an dauki matakin ne bayan samun koke da sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano kan zargin cin zarafin mukami da kuma bukatar gaggauta mayar da dukiyar gwamnati bayan barin aiki.
Yahaya ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikin kwamishinonin sun sayar da motocin gwamnati bayan sun sauka daga mukami.
Ya ce:
“Kadarorin gwamnati ba mallakar daidaikun mutane ba ne. Da zarar jami’i ya bar mukami, dole ne ya mayar da duk wata kadara ta gwamnati da ke hannunsa nan take.”
Ya kara da cewa: “Mun bi duk matakan doka tare da samun umarnin kotu kafin mu kwato motocin.”
A cewarsa, sun kwato motoci biyar daga mutane biyar, amma biyu ne kawai daga cikinsu motocin asali da gwamnati ta saya. Sauran ukun kuwa, bincike ya nuna an maye gurbin motocin asali da wasu daban bayan an sayar da su.
Shugaban hukumar ya musanta zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa, yana mai cewa aikin nasu ya ta’allaka ne kan kare dukiyar al’umma.
Ya ce: “Ba wai farautar kowa muke yi ba, muna kare dukiyar jama’ar Kano ne.”