Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojin Nijar sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 17 tare da kame...

Sojin Nijar sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda 17 tare da kame wasu 33

Sojojin Nijar sun kashe yan ta’adda 17 tare da kama wasu 33

Dakarun gwamnatin jamhuriyar Nijar sun sanar da kashe ƴan ta’adda 17 tare da kama wasu guda 33, inda kai tsaye aka miƙa su ga hukumomin da suka dace.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun ƙaddamar da wani samame ne kan ƙauyukan Niya da Damissa da kuma Garkouwa inda aka tabbatar da cewa masu laifin na samun mafaka a cikinsu.

Baya ga kashe masu laifin da kuma kama wasunsu, jami’an tsraon sun kuma kama gurneti guda 1,098 da kuma kilogram 48 na tabar wiwi da kuma kwayoyi masu sa maye sai kuma lita 23,250 na man fetur.

A cikin wannan mako kaɗai an samu rahoton wasu ababen fashewa har guda uku a sassan ƙasar, inda kwararru suka yi nasarar warware guda biyu, inda ɗaya kuma ya fashe amma kuma bai yi barna mai yawa ba.

A baya-bayan nan dai jami’an tsaron kasar sun matsa bincike da kuma harkokin tsaro musamman a kan iyakokin kasar, lamarin da ake ganin matukar ya ɗore ba shakka za’a samu saukin matsalolin tsraon musamman a ƙauyukan da ke iyakar ƙasar da makwaftanta.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments