Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMusulmi sun yi martani ga Amurka kan shawarar a soke shari'ar Musulunci...

Musulmi sun yi martani ga Amurka kan shawarar a soke shari’ar Musulunci a Najeriya

Majalisar koli ta harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) da sauran manyan kungiyoyin addini sun yi tir da kiran da wasu mambobin majalisar dokokin Amurka suka yi na neman soke shari’ar Musulunci a wasu jihohin kasar.

Wannan rahoto, wanda aka mika wa fadar White House, ya bukaci shugaba Donald Trump ya matsa lamba ga Najeriya don soke shari’a, tare da barazanar sanya takunkumi da haramta biza ga wasu ‘yan siyasa da shugabannin kungiyoyi kamar na Miyetti Allah.

A nasa martanin, sakataren NSCIA ya bayyana cewa shari’a tana daya daga cikin ginshikan addinin Musulmi a Najeriya kuma tana da kariya a karkashin tsarin mulkin kasar, Sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta fito fili ta nuna matsayinta na kare ikon kasar daga tsoma bakin kasashen waje.

A halin da ake ciki, kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci a bi matakan lumana tare da yin nazari kan tsarin mulki maimakon daukar matakan da za su iya haifar da tashin hankali tsakanin mabiya addinai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments