Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya bukaci majalisa ta hanzarta gyara kundin tsarin mulkin Najeriya

Tinubu ya bukaci majalisa ta hanzarta gyara kundin tsarin mulkin Najeriya

Shugaban Tinubu ya matsa lamba kan majalisa da ta hanzarta aiwatar da sauye-sauyen kundin tsarin mulki.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar kasa da ta fara shirin gyara kundin tsarin mulki domin samar da ’yan sandan jihohi a matsayin wani mataki na magance matsalolin tsaro a ƙasar.

Tinubu ya ce gyaran kundin tsarin mulki ya zama dole domin a kare dazuzzuka daga hannun masu laifi tare da amintar da ‘yan kasa daga tsoro.

Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa shugaban ya yi kira a sauya kundin tsarin mulki ne yayin wani buda-baki da ya yi da sanatoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

“Abin da na ke roƙo a yau shi ne ku fara tunanin yadda za a gyara kundin tsarin mulki domin kafa ’yan sandan jihohi, don mu kare ƙasarmu, mu karɓi dazuzzukanmu daga masu barna, mu kuma amintar da yaranmu daga tsoro,” Inji shugaba Tinubu.

Ya kuma yabawa sanatocin kan goyon bayan da suke ba shi wajen tinkarar matsalolin tsaro, yana mai alƙawarin cewa ba zai ɗauki haɗin gwiwarsu da wasa ba.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments