Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta ja kunnen yan kasuwa kan boye kaya da kara...

Gwamnatin tarayya ta ja kunnen yan kasuwa kan boye kaya da kara farashi a lokacin Ramadan

An gargadi yan kasuwa kan boye kayan abinci tare da kara farashi a lokacin azumi

Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa NOA ta gargaɗi ƴan kasuwa da su guji ɓoye kayan abinci da kuma ƙara farashi ba bisa ƙa’ida ba a lokacin azumin Ramadan.

A cikin wata sanarwa da babban daraktan hukumar, Lanre Issa-Onilu, ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa sun samu rahotanni kan yadda wasu yan kasuwa ke ɓoye muhimman kayan abinci da ake yawan amfani da su a lokacin azumi, domin su haifar da ƙarancin kaya a kasuwa da kuma ɗaga farashi.

Ya ce wannan dabi’a na kawo tangarda ga tattalin arziki, kuma ba ta da wata hujja, musamman a irin wannan lokaci da addinai ke jaddada tausayi, sadaukarwa da kuma sauke nauyin zamantakewa.

Shugaban NOA ya ƙara da cewa ɓoye kaya da gangan na kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arziki, haifar da tashin farashi tare da ƙara jefa iyalai cikin wahala a daidai lokacin da suke fuskantar ƙalubale.

Ya jaddada cewa yin kasuwanci cikin adalci da gaskiya wajibi ne, yana mai cewa daidaito da kuma rangwame a farashi sun yi daidai da ƙimar ƙasa da kuma koyarwar addinai.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments