Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAbdul Samad BUA ya zama na 4 a jerin mafi yawan arziki...

Abdul Samad BUA ya zama na 4 a jerin mafi yawan arziki a Afirka

BUA ya zama na hudu mafi arziki a Afirka bayan ya samu Naira tiriliyan 1.23 a rana daya

Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabi’u, ya samu karin dukiya da ta kai Dala miliyan 915 kimanin Naira tiriliyan 1.23 a rana ɗaya, lamarin da ya ɗaga shi zuwa matsayi na huɗu cikin attajiran Afirka.

Bisa ga sabon rahoton Bloomberg Billionaires Index, wanda ke bibiyar arzikin manyan attajirai na duniya a kullum, dukiyar BUA ta ƙaru da kashi 8.1 cikin ɗari, inda ta kai kimanin dala biliyan 12.3 zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2026.

Rahoton ya nuna cewa wannan ƙaruwa ta sanya shi ƙara matsawa gaba a jerin masu arziki a nahiyar Afirka, tare da nuna tasirin kasuwancinsa a fannin masana’antu da gine-gine.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments