Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumar ICPC ta binciki gidan El-Rufai da ke Abuja

Hukumar ICPC ta binciki gidan El-Rufai da ke Abuja

Hukumar ICPC sun dirar wa gidan El-Rufa’i don gudanar da bincike

Jami’an Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC sun binciki gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Abuja a ranar Alhamis.

Mai bai wa tsohon gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

A cewarsa, jami’an hukumar sun isa gidan El-Rufai inda nan take suka fara binciken dukkan sassan gidan.

Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya yi Allah wadai da matakin, yana mai cewa “binciken da jami’an suka yi ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya saba wa dokoki da haƙƙoƙin ɗan Adam.”

Tun a ranar Laraba hukumar ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana hannunta dangane da wani bincike da take yi.

Hukumar ba ta bayar da cikakken bayani kan irin binciken da ake yi a kansa ba.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments