Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa ana tunkarar wani lokaci mai matukar haɗari ga tsaro, da zaman lafiyar duniya, yayin da yarjejeniyar sarrafa makaman nukiliya tsakanin Amurka da Rasha ke daf da ƙarewa.
Antonio Guterres ya buƙaci Washington da Moscow da su gaggauta cimma matsaya kan sabuwar yarjejeniya, yana mai cewa ana cikin wani lokaci da haɗarin amfani da makamin nukiliya ya wuce ko wanne lokaci, cikin shekaru da dama da suka gabata.
Yarjejeniyar ta iyakance kowace ƙasa ga samar da makami mai linzami mai cin dogon zango 1500.
Rasha ta bayyana cewa yanzu babu wata doka da ta iyakance ta, amma duk da haka, za ta yi abun da ya dace.
Shugaba Trump dai tuni ya ce yana son sanya China cikin kowace irin yarjejeniya a nan gaba.