Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa gwamnatocin jihohi da kuma kananan hukumomi ne silar fadawar ‘yan Najeriya miliyan 133 cikin kangin talaucin da suke fama da shi a yanzu.
Wata sanarwa da hadimin shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X ce ta bayyana hakan, inda ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa jihohi da kananan hukumomi ikon samar da duk wasu bukatu na cire al’umma daga talauci.
Haka zalika ya ce babu wani sashe a kundin tsarin mulki da ya dora wa gwamnatin tarayya nauyin fitar da al’ummar Najeriya daga talauci, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma soki yadda ya ce gwamnatocin jihohi na watsi da muhimman ayyuka tun daga tushe irin su kiwon lafiya da kuma ilimi, tare da cewa hakan na ruruta wutar kangin talauci.