Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ziyarci wasu daga cikin mutanen Kurmin Wali da ke Karamar Hukumar Kajuru da aka ceto daga hannun masu garkuwa, a cibiyar kula da mata da yara ta Jihar Kaduna, inda suke karɓar kulawar lafiya bayan ceto su.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan na cikin sanarwar da Babban Mai Taimakawa Gwamnan Jihar Kaduna kan Kafafen Sadarwa, Abdallah Yunus Abdallah, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya kai ziyarar ne bayan samun ceto mutane 82 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, inda ya bayyana cewa ana ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin kubutar da sauran da ke hannun yan ta’addan.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya nemi a kafa sansanin soji a Kurmin Wali domin ƙarfafa tsaro a yankin, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa waɗanda aka ceto har zuwa lokacin da za su koma hannun iyalansu.