Jam’iyyar NNPP ta musanta rahotannin dake cewa jagoranta na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nemi kulla yarjejeniyar komawa APC mai mulki.
Wannan martani na zuwa ne bayan ficewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya haddasa jita-jitar cewa Kwankwaso ma ya yi yunkurin bin sa amma aka samu saɓani saboda wasu “tsauraran buƙatu” da ya gabatar.
Sakataren yaɗa labarai na NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya bayyana wa jaridar Punch cewa duk waɗannan zarge-zarge ƙarya ce tsantsa da nufin ɓata sunan tsohon gwamnan na Kano.
Ladipo ya jaddada cewa, Kwankwaso ya gana da Shugaba Bola Tinubu ne tun a shekarar 2024, kuma ba su taɓa tattauna batun komawa APC ba.
Ya kuma ce masu yaɗa jita-jitar suna yin hakan ne domin su raba Kwankwaso da sauran ƴan adawa masu ƙoƙarin haɗa ƙarfi da ƙarfe.
Ya bayyana Kwankwaso a matsayin mutum mai nagarta wanda ke yin siyasarsa domin amfanin talakawa, ba don neman muƙami ba.