Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKowanne Gwamna shi ne jagoran APC a Jihar sa - Tinubu

Kowanne Gwamna shi ne jagoran APC a Jihar sa – Tinubu

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa kowanne Gwamna shi ne jagoran jam’iyyar APC a Jihar sa

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnonin da ke ƙarƙashin jam’iyyar APC su ne jagororin jam’iyyar a jihohinsu daban-daban.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron karɓar Gwamna Agbu Kefas a hukumance zuwa APC da aka gudanar a Jalingo.

Da yake wakiltar Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, Tinubu ya sanar da cewa Gwamna Kefas ya karɓi ragamar jagorancin jam’iyyar APC a Jihar Taraba sakamakon ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

SourceICONIC FM
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments