Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa babu wani shiri, yarjejeniya ko tattaunawa da ke gudana a halin yanzu da za ta kai ga cire Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, daga kan sarautarsa.
Hakan dai ya fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, yayin wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya ce rahotanni da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta kan batun tsige Sarkin Kano ba su da tushe ballantana sahihanci.
A cewar Sanusi Bature, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba ta da niyyar tsoma baki cikin harkokin sarauta ta hanyar da za ta janyo rikici ko rashin zaman lafiya a jihar Kano.
Ya jaddada cewa gwamnatin na mutunta masarautu tare da kiyaye dokoki da al’adun da suka shafi harkokin gargajiya.
“Babu wata yarjejeniya ko shiri da zai kai ga cire Sarkin Kano.
Duk abin da ake yadawa jita-jita ne kawai,” in ji Sanusi Bature.