Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHarin Isra'ila ya kashe Falasdinawa 32 a Gaza

Harin Isra’ila ya kashe Falasdinawa 32 a Gaza

Aƙalla mutane 32 ne suka mutu sakamakon wasu hare-hare da jiragen yaƙin Isra’ila suka kai a zirin Gaza a ranar Asabar, a cewar hukumomin yankin.

Hukumomi a Gaza sun ce mata da ƙananan yara na daga cikin waɗanda aka kashe.

Sun ƙara da cewa, a wani harin jiragen yaƙi masu saukar ungulu sun yi luguden wuta a kan wani tanti da ke garin Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Falasɗinawa dai sun bayyana waɗannan hare-haren a matsayin mafi muni tun bayan da zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban Amurka Trump ya jagoranta a watan Oktoban da ya gabata ya fara aiki a farkon watan Janairu.

Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa an kai wasu hare-hare a matsayin martani kan abin bayyana a matsayin karya yarjejeniyar da Hamas ta yi a ranar Juma’a.

Isra’ila da Hamas dai na zargin juna da karya yarjejeniyar tun bayan da ta fara aiki a bara.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments