Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Usman Kusfah Rigi-Rigi, Ya Rasu

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Usman Kusfah Rigi-Rigi, Ya Rasu

Al’ummar Musulmi sun shiga jimami sakamakon rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Kusfah Rigi-Rigi.

Marigayi Sheikh Usman ya shahara wajen zurfin ilimin addini da kuma jajircewarsa wajen koyarwa da shiryar da al’umma tsawon rayuwarsa.

Ya sadaukar da kansa wajen yada koyarwar Musulunci, tarbiyyar dalibai.

Bayan samun labarin rasuwarsa, Musulmi daga sassa daban-daban sun rika yin addu’o’i, suna roƙon Allah (SWT) Ya gafarta masa kura-kuransa, ya jikansa.

Haka kuma, an yi addu’a ga iyalansa, dalibansa, da mabiyansa, domin Allah Ya ba su hakuri, juriya, da kwanciyar hankali a wannan mawuyacin lokaci.

Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanai game da jana’izarsa bisa koyarwar Musulunci ba.

Allah ya gafarta masa, ya jikansa, kuma ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus. Ameen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments